0
MAGANA JARI CE LITTAFI NA DAYA

labari na ashirin da biyu



LABARIN ANNABI SULEIMANU


Labarin Annabi Sulaimanu

      Wata rana Annibi Sulaimanu—tsira da aminci su tabbata gare shi—yana zaune, sai wadansu mata su biyu suka zo suka kawo kara a gabansa. Guda ta ce, “Ya Annabin Allah, da ni da wannan mace gida daya mu ke zaune. Na haifi da. Ana nan, bayan na haihu da kwana uku wannan mace kuma ta haihu. To, duk gidan ba kowa sai mu biyu kadai. Ran nan cikin dare ta kwanta bias danta ba ta sani ba, har ya mutu. Sai ta tashi da tsakad daren, ta dauki dana ta mayar wajenta, ta dauko danta mataccen ta kawo gabana, ni ko duk ban sani ba. Sa’ad da na tashi da safe garin in ba dana mama sai na gan shi mattacce. Da na duba da kyau, sai na ga she ba dana ba ne. Na gaya mata haka, ta ce karya na ke yi, mataccen ne dana. Muka yi ta gardama. Da muka ga abin zai kai ga barna, muka zo gare ka ka raba mana gardama, ya Shugaba.”

Waccan kuma ta ce, “A’a, karya ta ke yi, ya Shugabammu. Ni na riga ta haihuwa da kwana biyu, ran nan da dare ta taka nata ya mutu, ta zo ta musanya shi da nawa.”

Jama’ar da ke nan suka ce, “Kai, wanan shari’a ai ba ta warwaruwa, sai gobe ga Allah.”

Da Annabi Sulaimanu ya ji maganar matan nan sai ya sa aka dauko takobi aka zare, ya ce, “Tun da ya ke abin ya rikice haka, abu daya kadai za a yi a raba gardaman nan. Zan raa dan nan biyu ko wacenku ta dauki rabi, kowa ya huta, ku dangana har Allah ya sake ba ku wadansu.”

Da mace daya ta ji haka sai ta ce, “Don Allah kada a kasha shi. A ba ta, na yarda mata.” Amma waccan ta ce, “A’a, daidai ne, ya Annabi. A dai rabi shi, kowa ya huta.”

Da Annabi Sulaimanu ya ji haka sai ya ce, “Ku mika dan nan mai rai ga waccan da ta ce kada a kasha shi. Danta ne, ita ta haife shi.”

Da Musa ya ji aku ya yi shiru sai ya ce, “A’a! Yaya aka san wannan ke da da?”

Aku ya ce, “Haba, ba ka ga abin da a ke nufi ba? In da waccan ta haife shi ta ce a kasha shi tana kallo kiri-kiri?” Bai tsaya su Musa su sami damar fadin wani abu ba, sai ya ce, “Kafin ku kare tunanin wannan, tsaya ku ji yadda wani Sarki ya yi nasa hukuncin.”

Post a Comment

 
Top