0
ILIYA YA SAKE SHIGA





ILIYA YA SAKE SHIGA

 
DINAR SARKI WALDIMA.

A ranar da Iliya ya isa garin, ya tarar
Sarkli ya yi
kiran dina. Ya tara Sarakunan kasar,
da ya
yan Sarki, da malamai, da attajirai, da jarumai
wadanda suka yi wata bajinta. Ko
wadanne an
shirya musu rankin wurin zamansu
dabam.
Kowa ya shiga kayan ado masu tsada. Sarki da
Sarauniya kuma suna zaune bisa
kujeri a gefe
guda, sai barori ke raba abinci iri iri.
Da zuwan Iliya bai jira an yi masa iso
ba, sai ya fada cikin dakin dina. Bai zame ko
ina ba sai
wurin Sarki, ya dan sunkuyad da
kansa kadan,
kana ya zauna gab da shi. Waldima
bai gane shi ba. Ya dube shi kawai a maras
hankali, ya ce,
Na yi murna da ka sami dama ka zo
wurin
wannan biki da na shirya, don
manyan mutane, da jarumai, da attajirai. Zan sa a ba
ka wuri
daga can gefe guda. Za ka ci, ka sha
kyauta, ko
da ya ke ba ka daya daga cikin irin
mutanen da aka shirya dinar dominsu. Amma
kuma kai daga
ina ka ke? Mutumin wane gari ne? A
halin
wace zuriya ce kai?
Jin haka sai Iliya ya yi hushi. Ya dai tabbata babu jarumi kamarsa duk
cikin taron.
Sa an nan bai kamata Sarki ya
manta da shi
ba. Kuma kamarsa a ce a ware shi
wajie daya, ya kuma ci abinci kyauta! Sai ya ce,
Kai
Waldima, ni ne zan ci abincinka
kyauta! Ni za a
fada wa haka a cikin mata! Da fa
jaruman nan suka ji an ce musu mata, sai duk
suka dubi Iliya
da fushi. Daya daga cikinsu ys mike
ya ce,
Kai, Sarki ka ke fada wa wannan
magana? Karya ka ke yi. Ina ka ga mata a
nan, sai fa in
kana hauka ne! Zuciyar Sarki ta
harzuka, ya
kira jarumai shida, ya ce su fitar da
Iliya waje. Suna matsawa, Iliya ya zubad da su
matattu
duka. Sarki ya sake ce wa jarumai
goma su
kama shi. Su kuma an take Iliya ya
kai su lahira.
Wuri fa ya yamutse, kura ta yi sama,
sai
rincimi a ke yi. Aka tattaka wadansu
suka mutu,
wadansu suka gudu. Iliya ya fita abinsa, ya hau
dokinsa ya tafi kasuwar garin, ya
sayi abinci, ya
tara mutanen garin, yace su yi ta ci.
Wadansu
suka ce suna tsoron kada Sarki ya ji labari, ya
aiko a kama su. Iliya ya ce musu, Ku
yi ta ci
ba kome. Gobe war haka ni ne
Sarkin Birnin
Kib. Zan kuwa nada muku Sarautu. Saboda
tsoro, tilas suka ci abincin. Sai da
aka dade, sa
an nan suka sake jiki sosai, suka yi
ta kwasar
gara. Amma shi Iliya bai ci abincin ba, sai ya
tafi wani gida da a ke yin abincin
sayarwa, da
shaye-shaye iri iri, masu tsada, ya yi
tasa dinar
a can. Abin duniya fa ya sha wa Waldima
kai.
Ga dai gawar mutane hululu am bari
a gidansa,
ga shi yana jin yunwa bai ci abinci
ba, an kashe kuku da su boyi duka. Sai Waldima
ya leko, ya
tambayi wadansu mutane, ko sun
san mutumin
nan da ya yi musu wannan aiki. Sai
wani mutum ya ce, Allah ya ba ka nasara,
ai Iliya
ne, wanda ya taba zawa nan da
gagararren dam
fashin nan Gogaji. Sarki ya ce,
Haba, sai haka. Na san ba mai iya yin haka sai
shi! Sa
an nan ya tambaya ko wani zai iya
zuwa ya
rarraso shi ya zo da shi. Duk fadawa
sai kowa ya yi shiru, suna tsoron ransu. Can
sai wani ya
ce zai tafi. Da ya kusa da Iliya, sai
ya lababa ta
bayansa har ya kai kusa da shi, ya
ce, Ka zo Sarki na kira. Sai ya juya da gudu.
Iliya ya yi
shiru yana jiran ya ga wanda aka
aiko ya
kewayo ya fada masa, amma bai ga
kowa ba. Ya waiga bai ga kowa ba, sai ya ce,
Haka na
ke zato. Wane yaro, wane sunansa!
Da ya tsaya
da bai kai lahira ba.
Iliya ya aika wa Waldima cewa yana tafe, amma ya sa a yin shela tukuna
birni da
kauye duk kowa ya taru a kofar
fadarsa shi ma
zai yi tasa dinar. Masu yin abincin
sayarwa su kuma a fada musu duk su yi mai
kyau, mai
tsada, shi zai saye duk ya ba
mutane. Aka fada
wa Sarki. Nan da nan da rawar jiki,
ya sa aka yi shela, aka sanad da kowa da kowa
abin da Iliya
ke so ya yi. Har wadanda ba su taba
yin abincin
sayarwa ba, ran nan sun yi. Mutane
kuma har wadanda suka dade rabonsu da
zuwa birni, sun
zo. Filin fada dai ya cika makil. Iliya
da kansa
ya nuna wa kowa inda zai zauna. Ya
rarraba mutane kungiya kungiya, ya sa Sarki
daga can
gefe, kamar wani almajiri. Sa an nan
ya shiga
raba kayan dina. Da aka kare, Iliya
ya ce wa Sarki, To, yanzu fa na huce,
Tun kafin mutane su watse, sai Sarki
ya
mike ya ce a fada wa mutane, ya yi
murna da
wannan dina ta Iliya, amma yana so gobe a sake
taruwa zai yi wata dinar saboda
murnar zuwan
wannan bako.
Kashegari mutane suka sake taro
fiye da jiya. Sarki ya sa aka shirya dinar da
ba a taba
yin kamarsa ba a kasar. Aka shirya
wa kowace
kungiya wurin zamanta dabam. Sarki
da Sarauniya da Iliya kuma a ran nan
wurin
zamansu guda. Aka ci aka sha aka yi
ta
shagali. Can da Iliya ya ga giya ta
buge kowa a taron, har da Sarki, sai ya tashi
tsam, ya sulale
ya fita, ba wanda ya san inda ya
nufa. Don kada
ma a gane shi sai ya shiga irin ta
alhazai, ya nufi wani kauye kusa da Birnin Kib.
Da giya ta
saki Sarki, ya duba bai ga Iliya ba,
ya sa aka
dudduba ba a gan shi ba. Aka dai bi
sawu har hanyar dan kauyen nan, amma ba a
ga kowa ba
sai wani alhaji. Aka komo aka fada
wa Sarki.
Abin duniya ya rude wa Sarki, ya yi
zato ko Iliya bai huce ba ne.
Iliya bai tsaya ko ina ba sai wani
gida
inda a ke sayad da wata irin giya mai
tsada.
Wadda sai Sarakuna ke iya sayenta. Ya ce da
mai giyar yana so zai saya. Mai giya
ya dube
shi ya gan shi tsofai tsofai, ba
alamar anini tare
da shi, sai ya daka masa tsawa, Kai, dattijo,
tafi inda za ka tun da wuri, ai ba
irinkuy na ke
sayar wa da giya ba. Mutum ka tsufa
amma ba
ka san ka tsufa ba? Ka tafo da hanci duk
majina, ga tsumma, ka ce kana son
giya? To,
ba a sayar maka! Sai Iliya ya kara
marairaicewa ya rarrashi mutumin,
amma ya hana shi. Sai Iliya ya fadi ya lunshe
ido ya yi
kamar ya suma. Mutanen da ke
wurin suka ce
wa mai giyan nan, Idan ba ka ba shi
ba, zai mutu, ka ga ka jawo wata rigima ke
nan,: Aka
debo giya aka sa wa Iliya a baki, nan
da nan ya
farfado. Aka karo masa mai yawa
ya sha ya koshi, har ya bugu. Shi ke nan sai ya
shiga
kantin giya ya yi kwanciyarsa, ya yi
ta sharar
barci. Da dare ya yi kwarai masu
kantin suka ta da shi, ya ki tashi, sai suka rufe
kantin da shi
ciki.
Tun da asuba Iliya ya tashi, ya sa
kafa
ya buge kyauren kantin. A cikin kantin akwai
wadansu gangunan giya manya
manya, wadanda
kome karfin kato ba zai iya daga
ganga guda ba,
balle ya yi tafiya da ita. Iliya ya kwashi guda
uku, ya makale ko wace daya a
hammata, ya
rika tura daya da kafarsa, yana tafe
yana cewa,
Duk wanda ke so ya sha giya ya zo nan, har
wanda ba ya sha ma in yana so ya
zo. Daga
can masu giya sukaji, suka biyo shi,
suka yi,
suka yi, su kwace gangunan giyarsu, abu ya
faskara. Sai suka tafi suka kai kara
wurin
Alkali. Alkali ya aika aka rarraso
Iliya. Da jin
labarin, sai Waldima ya tsargu, ya tabbata ba
mai iya yin haka sai Iliya. Don haka
da zuwansa
sai ya ce, Haba Iliya, da ma ka
komo cikin
kamarka ta sosai. Sai Iliya ya bushe da dariya,
ya komo kamar yadda kowa ya san
shi. Ya biya
masu giya kudinsu, ya ba su sauran
giyar.
Da dare ya yi, bayan an gama hira, duk
fadawa sun watse, sai Waldima
kadai da Iliya,
Waldima ya ce masa, Ina so ka
taimake mu,
ka kubutad da mu daga sharrin wani rikakken
dan hari, maridi, wanda a ke kira
Falalu. Ko ina
ya ratsa cikin kasan nan sai ya rika
kwace, yana
raba mutane da dukiyarsu, ya kuma ba su
kashi. Ya dame mu kwarai, ba mu
kuwa da wani
wanda zai iya tararsa, sai kai kadai.
Iliya ya yi murmushi, ya gyara zama,
ya murza gashin baki, ya san ranarsa ta
zo, ya ce
wa Sarki, Allah ya ba ka nasara, an
gama.
Allah dai ya ba mu sa a. Ina so daga
cikin jarumanka, da ka ke takama da su
ka zabo mini
shida mu tafi tare. Amma mutanen
nan guda
shida ba don kome Iliya ya ke
bukatarsu ba, sai don ya jarraba jaruntakarsu.
Waldima ya umurci
jarumai shida su shiry su bi Iliya.
Da lokacin ya yi, jaruman nan suka
shirya, Iliya na gaba suna biye da
shi, suka nufi hanyaar da Falalu ke wucewa.

Post a Comment

 
Top