0
LITTAFIN ILIYA DAN MAI KARFI

shafin farko



ILIYA  DAN  MAIKARFI

GABATARWA DAGA MAWALLAFI

Salamu alaikum.

            Na shirya wannan dan littafi musamman don masu karatu su sami abin hira da debewar kewa.  Kamar yadda da mutane su ke da yawa, haka kuma ra ayoyinsu ya bambanta kan irin abubuwan da suka fi bukatar su karanta.  Wadansu sun fi so su ji labarai na ban dariya, wadansu kuwa labaran nishadi da alatu suka fi so.  Wadansu kuma sun fi bukatar labaran kasada da kuru, da dai sauransu.

            Daga cikin wadannan rabbai an ga akasarin mutanen da suka fi son jin labaran zaruntaka sun fi yawa.  Misali labaran su Sarkin Yaki Danwaire, su Kaura Ama, da Kaura Hausu, su Dambaskore da kamar su Kaura Wayya, su Kaura Isiyaku.  Wadannan jarumawa duka a kasan nan aka yi su.  Har yanzu kuwa labaransu su kan ta da tsimen matanen yanzu.

            Ganin ana bukatar jin irin wadannan labaru ya karfafa ni rubuta wannan dan littafi, na labarin wani shahararren mayaki da aka yi a zamanin da.  Wannan littafi ya kunsa kusan duk irin abubuwan da masu karatu ke bukatar su ji, watau ayyukan zaruntaka, da kasada, da shiga daular sarauta, da nishadi, da mamaki, har ma da ban dariya.  Ba shakka idan mai karatu ya kare karanta littafin nan zai fada cikin kogin tunanin al amuran duniya da suka shude.

            Ina fata wannan dan littafi ya biya bukatar da aka yi nufinsa da ita.  Ya zama sanadi ne na koyon karatu da rubutu ga wadanda ba su rigaya suka soma koyo ba.  Ya zama abin faranta zuciya ga wadanda suka karanta shi, ko suka ji an karanta shi.  Ya zama mabudi ne ga masu niyyar zama mawallafa ta hanyar dagawa.





                                                                        Salamu alaikum,

                                                                        Ni ne naku, 
                                                                             Ahmadu Ingawa.




    JERIN ABUBUWAN DA KE CIKI DAKI DAKI

 
  • ABIN AL AJABI 
  • GAMUWAR ILIYA DA WARGAJI  
  • ILIYA YA SHIGA DUNIYA
  • ILIYA YA GAMU DA GOGAJI  
  •  ILIYA YA SAKE SHIGA DUNIYA   
  • DINAR SARKI WALDIMA
  • ILIYA YA HADY DA FALALU  
  •  ILIYA DA YAN FASHI     ILIYA DA SARAUNIYA
  •  DINAR WALDINA TA UKU
  •  YAKIN ILIYA NA KARSHE    

Post a Comment

 
Top