0
 DUK DAD'INKI DA MIJI 






 DUK DAD'INKI DA MIJI


episode 45

 (BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


Na dade da dena zuwa makaranta ko da mammy ta tambayen don taji agun cousins dina nace mata raayi, taso ta tunkari Abba ya gwada mata tafita harkata babu ruwanta dani, nikuma agidan A.j babu sauki a alamarina, kullum duka, ga bana samun kwanciyan hankali sai innasamu cocaine, nazama very very addicted ranan a kitchen na yanki jiki na fadi, wallahy Adda haka A.j yazo ya tsallakeni da karuwarsa, basu bi takaina ba, kuma sai suka manta kofa a bude , makwabciyata wacce dama ta kawo insa mata kankara a fridge tashigo anan ihunta yafito dasu, bantaba sanar mata halin danake ciki ba hakan ya matukar bata mamakin ganin A.j yafito da wata, asibiti suka nufa dani anan yakira gidanmu, sai kace mutumin arziki, na rame nayi baki na lalace, Mammy ta ne tazo haka Abba na yarufe ido yace shi ya dade da yayeni donhaka babu mai sashi yazo, sauran yanuwa haka suka cika asibitin, likita anan ya sanar dasu shaye shaye yama kwanyata yawa, ina karama shekara sha takwas dinma yaushe nacika?, yakuma ce inbaayi hankali ba zan iyayin hauka, don bleading in brain nafarayi, sati na uku kafin nasamu sauki, anma duk dahaka baa sallameni ba, har lokacin Abba bai zo ba nayi kuka nayi takaici nayi nadaman auren A.j ada yakanje asibitin kullum yana makale, daga baya yadauke kafa sai ya kwan biyu baije ba, Adda ina gadon asibiti A.j yakara aure, lalle anyi gaskiya da wasu ke cewa MAI KUDI BAYA DARAJA SOYAYYA, basusan mutuncin shi ba ko da yake yagayamin amfani dani yayi baitaba sona ba, anma da ciwo, duk da bani zama cikin dadi anma na gwammaci wannan zaman akan da kishiya, adda don zan zama bora ne, abun gori, gani da kayan gori kala kala 



DUK DAD'INKI DA MIJI 


episode 46

(BASED ON A TRUE LIFE STORY) 


Muna zaune da Mammy yaya iby yashigo da katin auren A.j , baizata munsani ba don kuwa kuka nakeyi tsakanina da Allah Mammy ta kulu iya kuluwa tace " Ke inbanda ke, tun yaushe nake gaya miki Hafsat NAMIJI!! Kiyi taka tsantsan dashi, kin biyewa namiji kiga yadda rayuwarki ta dawo kin fifita namiji akan iyayenki" "Mammy amma sai yaga hallacin dana masa nabar iyayena saboda shi" ina kuka ina fada mata, wani dariya tayi sannan tace "toh ai duk DAD'INKI DA MIJI, DUK GATANKI DA MIJI SAI YA MIKI KISHIYA, kar kice ke kina zaune yana lailayaki kaman kwai ki hude ciki da hanci ko kice ya miki alkawari, shi din wa? Kika yarda? Balle nasan ke bawani dadin zaman kikeji ba toh akan me zaki yarda da kanki ki yaudare kanki akan son da yake miki ba zai iya miki kishiya ba? Ke waye? Na miji ubanki zai bashi gida da mota da aiki, amishi auren gata bashi zai hana ya danno miki kishiya ba, balle namijin dayasan son dakike mishi ya fi naki, yana da kudi a ajiye, me zai jira?, in ma kina tsammanin guarantee dinsa kinyi karya, hakanan suke gabansu fari bayansu baki, in zaki zage ki gyra kanki ki gyra aurenki da yafi miki komi, don kuwa Abbanki bazai bari ki zauna masa a gida da sunan zawarci ba, abunda baa taba yi a danginsu ba, kina ganinshi tsofai tsofai, aure ma nan baiyi da wuri ba haihuwarki ma ba da wuri ba, donhaka ki nutsu, wannan shaye shayen kidena, abun da zance miki kenan" yaya iby dake gefe ya ajiye katin auren hade da farar wasikar sannan yace "gashi inji maigidanki" hannu na rawa na karba ina karantawa, Adda takardan saki, saki uku!, ina gadon asibiti, yamin kishiya yasakeni! Uhm! Fada miki tashin hankalin dana shiga bata lokaci domin wani sabon jinya nafara ya damemu akan muje mu tattara kayana, haka aka kwashemun, Abba yace ba gidansa, Malam salisu yasa aka kai wani gida ya ajiye, yayinda nake jinya na, nayi kuka nayi bakin ciki na kuma yi nadama!, sai dana yi wata biyu a asibiti, randa aka sallamen ne nasan cewa Abbana babu mai kaifin zuciya da taurin kai irin nasa, domin kuwa rufe ido yayi yace karna dawo masa gida, gashi idda nakeyi toh, mammy tana kuka ina kuka yace maigadi inya barni nashigo abakin aikinshi, gida ya rude da tashin hankali, Anma daddy kyam yace ba gudu ba kuma ja da baya!, wallahi haka malam salisu yadaukoni mukayi abuja, yakaini gun wata lecturer tare suke aiki, yace nayi idda na agun,

Post a Comment

 
Top