0
DUK DAD'INKI DA MIJI





DUK DAD'INKI DA MIJI

 episode 31

(BASED ON A TRUE LIFE STORY)


 Saidu da ya juyo wani mari da ya bani, sai da naga taurari, alokacin nayi zaton ya Aliyu ne don shima haka yake zagewa yayi mari, dukka sosai saidu yamin sai da aka kwaceni, yakuma kira Alh. Ya sanar masa, nidai kam in banda kuka babu abinda nakeyi, bansan waya sanar da Ya umar ba ganin kiransa nayi, hannu na rawa na dauka yace "kizo gida yanzu kisamen" gabana ya tsinke na fadi, don na tabbata da zaa gwadani zaace jinina yahau, dasauri ina bugewa nafice na nemi keke nahau sai gida, yana zaune a kofar gida shida yaa Aliyu kaina a kasa nashige, ina shiga Umma na tarar a zaune tana kallo da murmushi ta taryeni hakan ya tabbatar min da bakomi, ima zama Ya umar yashigo nan yagayawa umma bari yamin magana ta tashi tafice, yarufo kofan falon shida ya Aliyu, Adda kinsan meya dauko?, wuka!, idonsa yayi jaa haka ya Aliyu suka zaunar dani "Dagaske ne kin kwanta dashi ko karya?" Ko nayi karya nasan yanzu Ya Umar zaice aje ayi test babu makawa nasan inadashi don haka kawai nayi surrender nace ae, Ya Aliyu da igiyan engine, dana markade ya hada, ya Umar ya daureni ajikin kujera daga ni sai vest sai underwear, yamin bulala a inda hankalina yadauka shine bulala 96, suma nayi anma ruwa suka yayyafo suka kara watsomin, Ya Umar yajanyo yatsan kafata yana kukan bakin ciki yace "kafan da zata kaiki ga aikata zina gwara na guntule" Adda inaji ina gani aka guntule min yatsa daya a kafata gashinan kina gani a guntule, alokacin umma dataji kuka na buga kofan takeyi da karfi suka ki bude mata saida suka gama ban kashi alokacin taci kuka tagaji, yaa umar yamata bayani bugun farko numfashinta ya tsaya, bamu nufi ko inaba sai asibiti, zan iya gayamiki soyayyar uwa domin alokacin duk radadin jikina, da rashin yatsa danayi wallahi na mike danaga mahaifiyata ahalin mutuwa, bamu isa asibiti ba umma tacika


DUK DAD'INKI DA MIJI 


 episode  32


 (BASED ON A TRUE LIFE STORY).


 Juyo da motan mukayi ina kuka kaman raina zai fita, Ya Aliyu ya kalleni cikin dacin rai yace "kin kasheta, saiki zuba ruwa akasa kisha, a iya sanina Hamdiya mahaifanmu basu da labari ko history marar dadi, sai kayi zina da dan wani zaayi da naka, mahaifinmu baiyi ba kinci amanar tarbiyar da yamiki, kisani cewa kema zaamiki" har muka isa kuka nake, alokacin ansanar da yanuwa da abokan arziki, aka mata wanka washegari dasafe aka kaita mazauninta, tunda naga mutuwan ummata duniya ta tsamemin akai, naga meye amfaninta bayan zamu mutu mubari, aranan Alh. Ya aikomin da takardan saki uku, ga kuma wasika ta Allah ya isa da sukamim shida iyalansa banbi ta kansu ba nabi takan rasuwan uwata ne, ran bakwai naga sammaci daga kotun musulunci, ana nemana, yayuna kuwa suka rufe ido sukace gwara amin hukunci dai dai ni, bazasu tsaya min ba, dama ga cutar HIV. Na lalace nayi baki shine kika ganni haka, yanzu dai kotu sun yankemin hukunci kamar yadda ake yankewa duk matar auren datayi zina, ajefeta, yanzu acikin satinnan zaamin insha Allah, mutane yanuwa sunsami Ya Umar ba yadda basuyi dashi ba yace da akan incigaba gwara arage mugun iri, labarina kenan, naga kafin na mutu yadace nazo nabaki keda makaranta ko zaa amfana, masu irin halina Allah yasa sudena, sannan ina rokon yanuwa da cewa da zaran kunga mace tana cikin wani hali don Allah karku mata baki, kumata adduan Allah ya shiryeta, kowa yanada boyeyyen jarabawa da kaddara, bawanda yafi kuma agun Allah, kana naka Allah na nasa, nasan nafada jarabawa anma abu mai muhimmanci anan shine ZINA cuta ne, sannan ZINA bashi ne, domin sai jiya wata take cemin ashe Alh. Umar yayi zinace zinace yana saurayi, gashi Allah daya tashi jarabbarsa yana ganin kaman yahaifi yaya maza ya tsira saigashi Allah yajuya alamari acikin gidansa, nagode sosai Adda da wannan daman" ta karasa tana goge hawaye, nima benaxir hawayen nake gogewa don nasha kuka sosai don tausaya mata, ba abunda yafi ciwo irin kasan kaidadun kwanakinka aduniya, na juya kan hafsat wato ceecee nace " zamu iya naki yau kuwa?, naga magrib tayi" "Ae mubari gobe zanzo, amma ga tsokaci ga yan makarantanki, nasan wasu iyaye yanzu akan labarin hamdiya bazasu ji shaawan kai yaransu jamia ba, inaso ince sucire wannan aransu, lalacewan Da duk inda yaga dama zai lalace, kinganni nan? Baa gwags na baci ba, tun kafin naje na lalace, a islamiyan gidanmu na fara shaye shaye, anan aka fara kawomin kayan maye idan anfita break a islamiya, sannan sanadiyata na shiga wannan halin NAMIJI ne, NAMIJI shiya yaudaren, NAMIJI shi ya wulakantani, NAMIJI shi yaci amanata, ya dizgani, babu abun yabo a tattare da NAMIJI"

Post a Comment

 
Top