0
 AURE KO ZAMAN GIDA ?

 

AURE KO ZAMAN GIDA ?

••••••PART 3••••••

…Abinda yasa naqi zuwa kuwa kiranshi maman
jamila (kishiyar maman mu) tace koda ban saida
tallan da ta dauramin ba kada in kuskura wani ya
bani kudi yamun juye ko in bishi gida duk ranarda
nayi haka sai ta yankani,Kuma zata riqa dukana
kamar yanda take dukansu jamila (yayanta
kenan )Ashe su jamila juye suke ana ta6a lalubarsu
shiyasa take chin ubansu.. naceto, Zo karakani muje
tare har yace bazai jeba sai kuma yace kawo
inkaimuki na bashi ya kai ya dawo yace waranki na
dari shida da talatinne ga kudin kikai wa almajirai
waran. Yace min ko ki saida rabi kikaiwa almajirai
rabi ki boye sauran kudin. Har na yarda da
shawaransa sai kawai naga idan maman jamila
tagane zataci ubana tace ina nake samun kudi,
Nakoma gida da wuri akace ya akayi nadawo da
wuri nayi bayani tace kar dai in kuskura in shiga
motarsa kuma duk abinda ya bani kar inci, Nace to,
Tun daga ranar idan nafito talla nan zan tarar da
motar mutuminnan nan kuma zan barta, Banta6a
zuwa jikin motanba sai na jira audu abokin tallana
yazo yakai asaye abani kudi...

Yanzu babana ya chanza yana bamu kulawa sosai
kuma ya sakamu islamiya dukanmu, Inada qoqari
sosai amma su jamila sai a hankali cikin shekara
daya na sauke qur'ani nashiga bangaren
hadda,Namma banyi qasa a guywaba wata tara na
haddace qur'ani da tajwid da komai, Nice tafarko
atarihin makarantarmu da ta haddace qur'ani cikin
wata tara dama tun lokacinda nake karatu kamin in
iya na haddace shiyasa da nazo sai yamin sauqi
nandanan na haddace, Akayi gagarumin bukin yaye
dalibai hadda shugaban makarantarmu yazo nay
karatu da muryar nan tawa nasamu kyaututuka
sosai agurin malamanmu da manyan baqi, Yanzu na
daina talla saboda baba yana iya bakin qoqarinsa
yachanza sosai yanzu baya barinmu da tsumma
kamar da mun wadata sosai, Ranar nadawo daga
islamiya baba yace inzo naje gunsa sai yacemun
wai aure zai nida ko nono banida za'ayimin aure gani
da qaramin jiki saboda ta dade da fara nono amma ni
yar qwaila dani, Bance komaiba nace to, ko kinada
wanda kikeso nace a'ah, Aka sa ranar aurena aka
dauramin aure da mijin da banta6a ganiba bansan
ko waye shiba…
Kukasance tare dani a 

 
AURE KO ZAMAN GIDA?

PART 4

…Iya tunanina aurena da wani dan mashukurin mai
kudi rana daya akayi shi dan jama'ar da suka taru
sunfi qarfin suzo aurena amma daga qarshe
mungane gurin auren nawa sukazo,Har bayan
daurin aurena ina gidanmuban tareba, Bana fita ko
ina, Sai taya maman jamila aiki, Ke in gayamaki jabo
wllhy saida nayi shekara biyar agidanmu ba miji ba
labarinsa kuma ba zancen tarewa, Har na balaga,
Ba miji inason inyi magana amma kunya ta hanani
yin magana duk qannena mata jamila da hafsatu an
musu aure jamila da wani har ta haihu da wani ciki
ajikinta hafsatu kuma da cikinta tsoho, Nigani agida
farko abin baya damuna kuma sam ban fuskantar
tsangwama agurin maman jamila, Yanzu na girma
nasan miye aure saboda ina zuwa wata islamiya
dadare ta matan aure a unguwarmu, Inajin
abubuwan da ake koya mana mata da wuri suke
zuwa dan suyi ta tadi, Mijina kaza mijina kaza nidai
bana ce musu komai, Abin duniya ya isheni nayanke
shawarar zan yiwa baba magana sai dai kuma
kunya nakeji nace ko infara yiwa maman jamila
maganane inji abinda zatace, Haka kuwa akayi, Ina
biya mata karatun qur'ani bayan munqare muna hira
saina cemata wai maman jamila waye mijina..? Naji
kamar bata jini ba namaimata tambayar, Ta d'ago
ido ta kalleni tace mun kitambayi babanki, Nayi shiru,
Ban qara cewa komaiba, Munqare karatu da ita na
shige daki, Sai tunani kala kala nakeyi gaskiya
inason sanin miye matsayina matar aure ko
bazawara? Zaman aure nake ko zaman gida?
Shekara biyar ba miji ba labarinsa sai wani niqab da
baba yasani sakawa tunda aka dauramin aure, Yan
kwanakinnan nashiga damuwa sosai sai nake
tunanin ko dan banida uwane aka yimin haka, Lallai
maraici hadarine, Nashiga rera kuka mara sauti nayi
wata biyu Kullum sai nayi kuka duk wata walwala ta
gushe mini banida aiki sai tunani da damuwa nashiga
tsaka mai wuya narame, Na kode, Nayi baqi, Duk
wata halitta ta jikina saida ta chanza..

 Na yi alwashin
zanyiwa babana magana, Bayan yadawo daga
kasuwa nace inada magana dashi yace to naje
gurinsa, Inson inyi magana sai muryata ta fara rawa
bansan lokacinda kuka ya subucemin ba nayi kuka
sosai baba ya rasa gane kaina gashi ba kowa
agidan saini nima dan banje islamiya bane, Daqyar
nasamu nayi shiru amma nakasa tambayarsa, Can
baba yace nasan zaki damu ace shekara biyar da
watanni da daura miki aure amma bakisan mijinkiba.!
kuma baki tare Gidankiba ba ,Amma kiyi haquri
nasan banmiki adalciba, Nafarko ban baki damar
zabar mijin da ranki yakesoba ban tambayi
ra'ayinkiba inji shin kina sonsa ko yaya,! Bakisan
wayeba bakisan komai akansaba hasalima bakisan
wayeshiba ban barki kinyi karatun bokoba, Sannan
shekara biyar dai dai da rana daya bakimin magana
ba Allah yayi miki albarka kuma mijinki wannan
shekarar zai dawo insha Allah, Idan ya dawo tare
gidanki tashi kije ki kwanta Allah yayi miki albarka,
Koba komai raina yayi sanyi najin cewa mijina zai
dawo wannan shekaran dan wllhy na gaji da zama
da igiyar aure akaina…

Post a Comment

 
Top